Zargin almundahana: Hukumar ICPC ta ci gaba da bincike duk da janye ƙorafin Dangote

dangote icpc faruk2

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa ICPC ta bayyana cewa za ta ci gaba da binciken ƙorafin da Alhaji Aliko Dangote ya shigar kan tsohon shugaban hukumar kula da harkokin mai da kayyade farashi ta ƙasa NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, duk da cewa mai ƙorafin ya janye takardar ƙorafin.

A wata sanarwa da kakakin ICPC kuma shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mista J. Okor Odey, ya fitar, ya bayyana cewa hukumar ta karɓi wasiƙa daga lauyoyin Dangote da ke sanar da janye ƙorafin, amma hakan ba zai hana ci gaba da bincike ba.

Dangote ya shigar da ƙorafi kan Farouk Ahmed bisa zargin cin hanci da almundahana, inda ya zarge shi da ɓarnatar da kuɗaɗe da kuma kashe Miliyoyin Daloli wajen karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu masu tsada a ƙasar Switzerland.

Haka kuma, ƙorafin ya zargi Farouk da tauye bunƙasar harkokin tace man fetur a cikin gida ta hanyar haɗin gwiwa da ’yan kasuwar ƙasashen waje da masu shigo da mai, su ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai daga waje.

Karanta: Zargin cin hanci: ICPC ta gayyaci Aliko Dangote kan ƙorafin da ya shigar na tsohon shugaban NMDPRA

Ƙorafin ya kuma nuna cewa an kashe fiye da Dala Miliyan Bakwai ba tare da hujjar halaccin tushen kuɗin ba, lamarin da Dangote ya ce ya nuna rayuwa fiye da ƙima da ya dace da ma’aikacin gwamnati.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ICPC ta bayyana cewa bincike ya riga ya fara tun kafin karɓar sanarwar janye ƙorafin, don haka binciken zai ci gaba bisa tanadin doka domin kare muradun al’umma da ƙasa.

Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da aikinta na doka ba tare da katsalandan ba, tare da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here