Zaben 2023: Wani jigon APC ya shawarci Tinibu da ya barwa Osinbajo takara

Bola Ahmed Tinubu 678x381 1
Bola Ahmed Tinubu 678x381 1

Tsohon mashawarcin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Borno, Sanata Muhammed Abba Aji ya shawarci jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa tare da kyale mafarkansa ga ubangidansa na siyasa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

A wata hira da aka yi da shi ranar Litinin a Abuja, Abba Aji, dattijon Arewa wanda ya kasance tsohon mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dokoki ya jaddada cewa duk da kalubalen da ake fuskanta, Osinbajo yana da kwakkwaran tushe na goyon bayan Arewa, tare da dimbin magoya bayansa a fadin kasar.

Sanata Abba Aji wanda daya ne daga cikin dattawan Arewa a kungiyar Progressive Consolidation Group PCG, wata kungiya mai rajin tabbatar da ra’ayin Osinbajo tun a shekarar da ta gabata, ya kuma yaba da bikin ba zato ba tsammani da aka yi a fadin kasar baki daya na murnar ayyana Farfesa Osinbajo a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023.

Yace; “Na shiga siyasa tun farkon shekarun 1980 kuma zan iya gaya muku cewa al’ummar Najeriya a halin yanzu sun fi wayewa fiye da yadda kuke da su a baya.

Zanga-zangar ba zato ba tsammani wata Yar manuniya ce dake tabbatar da ikon mutane kuma hakan yana nuni da kyakkyawar damar da Farfesa Yemi Osinbajo ke da ita ta samun nasara a zaben,” in ji shi.

Da yake karin haske, Sanata Abba Aji ya bayyana Tinubu a matsayin babban jigo a jam’iyyar da ya kamata a ce an tabbatar da cewa kyakkyawan ra’ayin da aka kawo wa Osinbajo ya ci gaba da bunkasa.

“Tinibu babban jigo ne a jam’iyyarmu kuma ya taka rawar wajen ganin an samu mataimakin shugaban kasa Osinbajo, kuma ya burge shugaba Buhari da miliyoyin ‘yan Najeriya.

“A matsayinka na jagora, idan ka kawo babban ra’ayi, ya kamata ka kyale irin wadannan su kara girma kuma sanarwar nuna sha’awa da mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi a zaben shugaban kasa mai zuwa alama ce ta ci gaba mai inganci kuma mataki na gaba shi ne Osinbajo ya karbi shugabancin kasa a 2023. inji Abba Aji

Da yake tabbatar da cewa Osinbajo na da kyakkyawar dama ta lashe zaben shugaban kasa, Sanata Abba Aji ya jaddada cewa matsalar tsaro a jiharsa ta Borno ta samu raguwa sosai a karkashin gwamnatin Buhari, inda ya kara da cewa Osinbajo ya burge ‘yan Najeriya matuka da irin ayyukan da ya yi a tsawon lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban Kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here