Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na’Abba, ya rasu a Abuja yana da shekaru 65 a duniya.
Mista Ahmed Tijjani Lawal, mai taimaka wa marigayin ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Laraba a Kano.
Ya ce kakakin na 8 ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba a babban asibitin kasa dake Abuja.
Na’Abba ya zama dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben majalisar dokoki ta kasa a watan Afrilun 1999 a mazabar Kano Municipal Kano State.
Ya bar mata daya, ’ya’ya 10, da jikoki uku..
“A yanzu haka muna shirye-shiryen kai gawar Kano domin binne gawar a yau.” NAN













































