Za a samar da ƙarin wasu manyan makarantun gaba da sakandare bakwai a Zaria a 2025 – Kakakin Majalisa

Tajudeen Abbas 695x430

Kakakin Majalisar Wakilai, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce mazabar Zariya za ta samu karin cibiyoyin ilimi na gwamnatin tarayya guda bakwai a cikin kasafin kudin 2025.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Tajuddeen ya bayyana hakan ne a lokacin buda baki na Ramadan da aka gudanar a Zariya a ranar Asabar.

A cewarsa, an yi hakan ne domin kara daukaka martabar Zariya a matsayin cibiyar ilimi mai zurfi.

Kakakin ya zayyana cibiyoyin da suka hada da Kwalejin Aikin Gona ta Tarayya, Cibiyar Kula da Dabbobi ta Tarayya da Kwalejin Fasaha ta Tarayya.

Karin karatu: Majalisar dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni 6

Sauran sun hada da Cibiyar Bunkasa Gudanarwa, Cibiyar Inganta Fasaha, Makarantar Nakasassu (Firamare da Sakandare) da Sabbin Makarantun Sakandare na Tarayya guda hudu.

Tajuddeen ya ba da tabbacin cewa za a aiwatar da wasu ayyukan raya kasa wadanda ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma a cikin kasafin kudin shekarar 2025.

Tajuddeen ya yaba da irin hadin kai da goyon bayan da ‘yan mazabar suka ba shi wanda a cewar sa, shi ne tushensa na samun sakamako a majalisar dokokin kasar.

Sai dai ya yi kira da a yi wa shugaban kasa Bola Tinubu addu’a, inda ya kara da cewa irin wannan na iya taimakawa gwamnati da kasar nan wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma bunkasa tattalin arziki.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma, Alhaji Garba-Datti Babawo, ya yaba wa shugaban majalisar kan yadda ya dauki kowane dan majalisa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko yanki ba.

Babawo ya bukaci Tajuddeen da ya ci gaba da gudanar da kyakkyawan salon shugabancinsa wanda ke saukaka zaman lafiya, ci gaba da kuma dangantaka mai kyau a cikin majalisar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa fitattun ‘yan siyasa, malamai, shugabannin gargajiya, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a mazabar tarayya ta Zariya, sun kada kuri’ar amincewa da shugaban majalisar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here