Rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ta kama wasu mutane uku bisa zargin sayen wata mota kirar Mercedes-Benz GLE ta Naira Miliyan 75 ta hanyar amfani da biyan kuɗi na bogi.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Ibrahim Tijjani, Jamilu Auwal da Mohammed Nura Dauda, inda ake zarginsu da yin amfani da wannan dabarar wajen mallakar motar ba bisa ka’ida ba.
An kama su ne a ranar 28 ga Janairu, 2026, a unguwar Kabuga da ke cikin birnin Kano, bayan binciken da rundunar ’yan sandan jihar ta gudanar.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano ranar Asabar.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen sun sayi motar ne daga Gwarinpa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, inda suka biya kuɗin ta da alert na bogi da wani Ibrahim Yahaya ya tura, wanda har yanzu ya gudu ba a gani shi ba.
Rundunar ’yan sanda ta kwato motar, tare da miƙa ta ga rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jajircewa da kwarewa, tare da kira ga al’umma da su kasance masu sa ido da kuma kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa domin daukar mataki cikin gaggawa.












































