‘Yan Bindiga sun sace wani Hakimi a Kaduna

'Yan bindiga, sace, Hakimi, Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin Tunburku da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, Malam Ashiru Sherehu. An ce an yi garkuwa da Sherehu ne a...

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin Tunburku da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, Malam Ashiru Sherehu.

An ce an yi garkuwa da Sherehu ne a lokacin da yake dawowa daga gonarsa a ranar Asabar.

‘Yan bindiga sun addabi garin, wani yanki na gundumar Fatika a ‘yan kwanakin nan.

Karin labari: “Abinda ya sa na ki karbar cin hancin naira miliyan 150 daga wani dan kasuwa” – Dan Sanda

A cewar Ahmadu, wani mazaunin yankin, manoma ba sa iya shiga gonakinsu da ke da nisan kilomita kadan daga garin saboda tsoron kada a kashe su ko kuma a sace su.

Hussaini Umar, wani basaraken gargajiya a yankin kuma Sarkin Fadan Galadimawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da hakimin kauyen da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar.

“Ya na dawowa daga gonarsa da ke unguwar Tunburku sai ‘yan bindigar suka tare shi suka tafi da shi. Har yanzu ba mu ji ta bakin wadanda suka sace shi ba, ba su tuntube mu ba,” inji shi.

Karin labari: Tsohon babban hafsan tsaron kasa Ogohi ya rasu

A cewar Hussaini, an sace wasu manoma biyu a Sabon Layi da ke karkashin gundumar Kidandan a lokacin da suke aikin gonakinsu a ranar Lahadi da rana.

Ya bayyana cewa mutanen kauyen da lamarin ya faru a gaban su sun kasa shiga tsakani saboda ‘yan bindigar na dauke da muggan makamai.

Umar ya koka da yadda ‘yan bindiga ke farautar manoma.

Karin labari: Gwamnatin jihar Kano tayi mana rinton aiki – APC

Ya yaba da kokarin sojojin da aka tura yankin amma ya roki gwamnati da ta aike da jami’an tsaro da yawa saboda matsalar rashin tsaro.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan lamarin ba. Kiran da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan, bai amsa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here