Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa an kashe fitaccen ɗanbindigar nan da ya yi fice wajen garkuwa da jama’a don neman kuɗin fansa, wato Kachalla Isuhu Yellow.
Lamarin ya auku ne da yammacin ranar Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami’an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewacin ƙasar.
Ɗanjarida mai bincike kan harkokin ƴanbindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗanbindigar.
Isuhu ya fi yin fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar ɗanbindigar a wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar.
Sanarwar ƴansanda ta ce jam’ian tsaro ne suka samu labarin cewa an ga ƴanbindiga da dama ɗauke da muggan makamai sun nufi garin Keta, inda ya ce jami’an tsaron haɗin gwiwa na ƴansanda da askarawan Zamfara da ƴan sa-kai da mafarauta suka kai ɗauki, inda suka fafata da gungun ƴanbindigar na tsawon lokaci.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe ɗan sanda ɗaya, da askarawan tsaron jihar guda huɗu da ƴan sa kai guda biyu, sannan mafarauta biyu sun jikkata a lokacin artabun.
“Amma duk da haka jami’an haɗin gwiwar sun samu nasarar kashe ƴanbindiga da dama, ciki har da fitaccen ɗanbindiga Ɗan Isuhu Mudale, wanda ya daɗe yana addabar yankin Tsafe,” kamar yadda sanarwar ta nuna.