Wani hari da ake zargin ƙungiyar ‘yan bindiga ne suka kai a ranar Laraba 28 ga watan Janairu, 2026, ya jefa al’ummar Durmawa da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Jihar Kano cikin jimami bayan an harbe wani mutum har lahira a bainar jama’a.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa marigayin, Alhaji Habibu Muhammad, ‘yan bindiga ne suka kai masa hari yayin da suka iso a kan babur, irin hanyar sufuri da ake yawan amfani da ita wajen aikata laifuka a yankin.
Matar marigayin, Rafi’atu Adamu, ta bayyana cewa maharan sun tare mijinta ne yayin da yake gudanar da harkokinsa na yau da kullum, inda suka kwace wata jaka da ake zargin tana ɗauke da kuɗi masu yawa, kafin su harbe shi.
Ta bayyana cewa makwabta ne suka sanar da ita abin da ya faru bayan sun ruga zuwa gidanta cikin firgici, inda suka gaya mata cewa an harbe mijinta.
Bayan ta isa wajen, ta tarar da shi kwance babu rai, lamarin da ya kasance mafi muni a rayuwarta.
Rafi’atu Adamu ta ce mutuwar mijinta ta bar ta da nauyin kula da ‘ya’yansu tara ita kaɗai ba tare da tabbataccen tushen samun kuɗin shiga ba, lamarin da ya sa yanzu take ɗaukar nauyin uwa da uba a lokaci guda.
Ta yi kira ga gwamnatin Jihar Kano, hukumomin tsaro da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su taimaka mata, domin tana bukatar kariya, tallafin kuɗi da kuma damar farfaɗo da rayuwarta da ta ‘ya’yanta.
Kisan Alhaji Habibu Muhammad ya sake jaddada matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a wasu sassan Jihar Kano, inda al’umma ke ci gaba da kira ga daukar tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.













































