HOTUNA: Khalifa Muhammadu Sanusi na II Ya kaiwa Sanata kwankwaso ziyarar ta’aziyyar kaninsa

FB IMG 1641458660890
FB IMG 1641458660890

Sarkin Kano jinin Fulani na 14, Mallam Muhammad Sanusi Na II Ya ziyarci Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin yimasa ta’aziyyar rasuwar dan uwan sa Kwamaret Inuwa Musa kwankwaso

Idan za a Iya tunawa, Dan Uwa ga Tsohon Gwamnan ya rasu ne aranar 20 gawatan Disamba shekarar Bara ta 2021 bayan Fama da rashin lafiya a asibitin koyarwa na Mallam AMINU Kano Dake Kano.

Mal. Muhammad Sanusi na II, Wanda shine jagora Kuma babban Halifan darikar Tijjaniya na kasa, yayi Adduar neman gafara ga mamacin tareda baiwa Yan uwa da iyalai hakurin jure wannan babban rashi

Da yake maida jawabi, Sanata kwankwaso ya godewa mal. Muhammad Sanusi na II da Yan tawagar sa bisa kawo masa wannan ziyarar ta’aziyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here