Tsohon babban hafsan tsaron kasa Ogohi ya rasu

Ibrahim, Ogohi, tsohon, babban, hafsan, tsaron, kasa, rasu
Tsohon babban hafsan tsaron kasa, Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu. Ogohi ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya. A cewar majiyoyi, ya shafe makonni da...

Tsohon babban hafsan tsaron kasa, Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu. Ogohi ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

A cewar majiyoyi, ya shafe makonni da dama yana fama da rashin lafiya da suka shafi shekaru kafin ya rasu a gidansa da ke Abuja da sanyin safiyar Lahadi.

“Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu ne a ‘yan mintoci da suka gabata, da safiyar Lahadi,” yayin da wani dan uwa ya tabbatar da labarin rasuwar.

Karin labari: Gwamnatin jihar Kano tayi mana rinton aiki – APC

Marigayi Admiral ya kasance babban hafsan tsaro tsakanin 1999 zuwa 2003.

Shi ne babban hafsan sojan ruwa na farko da ya kai matsayin tauraro hudu a rundunar sojin Najeriya, ciki har da kasancewarsa babban hafsan hafsoshin sojan ruwa na farko.

Marigayi babban hafsan tsaron ya fito ne daga Okura, Lafia a karamar hukumar Dekina a jihar Kogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here