Tinubu zai kai ziyarar aiki Katsina ranar Juma’a – jami’i

Tinubu Bola 750x430

A ranar Juma’a ne shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwana daya jihar Katsina.

Dakta Bala Salisu Zango, kwamishinan yada labarai na jihar ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba a Katsina.

Ya ce shugaban zai kaddamar da ayyuka guda biyu daga cikin dimbin ayyuka da gwamnatin Dikko Radda ke jagoranta.

Kwamishinan ya ce, ayyukan da aka samar don kaddamar da su sun hada da Eastern Bypass, wanda ya taso daga titin Dutsin-ma, ta hanyar Kano da Daura, kuma ya kare a Yandaki, a karamar hukumar Kaita.

Karin karatu: Gwamna Kano ya amince da biyan Naira Biliyan 15.6 ga tsofaffin kansilolin APC sama da 3,000

A cewarsa, shugaban kasar zai kuma kaddamar da cibiyar sarrafa kayayyakin gona ta jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa ziyarar za ta kasance ta farko da shugaban kasa zai kai jihar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Salisu Zango ya bayyana cewa ziyarar za ta kuma zama wata dama ga jihar domin tattaunawa da shugaban kasa kan wasu kalubalen da take fuskanta musamman rashin tsaro.

Don haka kwamishinan ya bukaci mazauna jihar da su fito baki daya domin tarbar shugaban kasa da kuma zama masu bin doka da oda. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here