Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida najeriya daga kasar Ingila.
Daya daga cikin mai magana da yawunsa Festus Keyamo ne ya tabbatar da dawowar tsohon Gwamnan na Legas ta hanyar sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Keyamo ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Mikiya ta sauka.
“Dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya dawo Abuja daga Landan.”
Tinubu ya shafe akallaMutsawonkwanaki 12 a Landan tare da wasu makusantan sa dacewa sun je Landan ne domin hutawa.












































