Sojojin Najeriya sun binne gawarwakin dakaru 22 da aka kashe a Neja

Burial Of Beechcraft King Air 350 Crew Holds In Abuja
Burial Of Beechcraft King Air 350 Crew Holds In Abuja

Rundunar sojin Najeriya ta binne gawarwarkin dakarunta 20 da ‘yan bindiga suka kashe a wani kwanton-ɓauna da suka yi musu a jihar Neja.

A makon da ya gabata sojojin suka ce dakarunsu 36 aka kashe a ani kwanton-ɓauna da ‘yan ta’adda suka yi musu a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina, sannan kuma da faduwar wani jirgin yaƙin sojin a yankin Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Rahotonni sun ce jana’izar ta samu halartar ministocin tsaron kasar biyu Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, tare da babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christopher Musa.

Sauran manyan baƙin da suka halarci jana’izar sun haɗar da babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, da babban hafsan sojin ruwa na ƙasar da sauran iyalan gwarazan dakarun da suka mutu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here