Lokacin da Yoweri Museveni ya karɓi mulki a Uganda a shekarar 1986, ya bayyana cewa matsalar Afirka gaba ɗaya da Uganda musamman ba ta mutane ba ce, illa shugabannin da ke son dawwama a kan mulki.
Sai dai a yanzu shugaban ƙasar mai shekaru 81, wanda tsohon jagoran ‘yan tawaye ne, na neman wa’adi na Bakwai a zaɓen da za a yi ranar Alhamis, bayan kusan shekaru Arba’in yana jagorantar ƙasar da ke gabashin Afirka, inda yawancin ‘yan ƙasar ba su taɓa sanin wani shugaba ba face shi.
Museveni ya hau mulki ne cikin yanayi na fata da kyakkyawan zato bayan ya jagoranci gwagwarmayar hambarar da gwamnatocin kama-karya.
Sai dai cikin ɗan lokaci, wannan kyakkyawar fahimta ta dusashe sakamakon zarge-zargen cin hanci da mulkin danniya.
Masana siyasa sun nuna cewa cin hanci ya kasance ginshiƙi a tsarin mulkinsa tun daga farko, kodayake Museveni ya amince cewa wasu jami’an gwamnati sun aikata laifuffukan cin hanci, yana mai cewa duk wanda aka kama ana gurfanar da shi gaban shari’a.
A matakin ƙasashen waje, Museveni ya gina alaƙa da ƙasashe masu ƙarfi ta hanyar rungumar manufofin tsaro na ƙasashen yammacin duniya.
Ya tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa wuraren rikici kamar Somaliya da Sudan ta Kudu, tare da karɓar dubban ‘yan gudun hijira zuwa Uganda.
A cikin gida kuwa, tarihin mulkinsa ya kasance mai gauraye tsakanin nasarori da matsaloli.
Gwamnatinsa ta samu yabo wajen yaƙi da cutar kanjamau da kuma murƙushe ƙungiyar ‘yan tawaye ta Lord’s Resistance Army da ta addabi ‘yan Uganda na tsawon kusan shekaru ashirin.
Amma yawaitar cin hanci ya raunana ayyukan gwamnati, inda rahotanni suka nuna cewa yara kaɗan ne ke kaiwa matakin sakandare bayan fara firamare, yayin da ayyuka masu albashi mai kyau suka zama abin wahala ga mutane da dama.
A tarihi, Museveni ya taka rawa a fafutukar da ta kai ga korar Shugaba Idi Amin, kafin Milton Obote ya karɓi mulki a 1980, sannan aka kifar da shi a juyin mulkin 1985.
A shekarar 1986, reshen sojan ƙungiyarsa ta National Resistance Movement ya hambarar da Tito Okello.
Daga baya, yunƙurinsa na jawo jarin waje, kafa doka da oda, da inganta rayuwar jama’a sun samu karɓuwa a ƙasashen yamma, amma ci gaban tattalin arziƙi ya zo da ƙarin fushin jama’a kan cin hanci.
A ƙarƙashin shirin keɓance kadarorin gwamnati, an sayar da kamfanonin gwamnati da dama ga ‘yan uwa da makusantan Museveni da farashi mai rahusa, lamarin da ya jawo zarge-zargen almundahana.
Museveni ya lashe dukkan zaɓukan shugabancin ƙasa guda shida da ya tsaya, ciki har da waɗanda ya fafata da Kizza Besigye, wanda aka kama a 2024 kuma ake tuhumarsa da cin amanar ƙasa.
A 2005, majalisar dokoki ta soke iyakar wa’adin shugabanci, matakin da masu suka suka ce an yi shi ne domin ba shi damar ci gaba da mulki ba tare da iyaka ba.
Masu adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓe bisa zargin maguɗi, amma hukumomi sun musanta hakan tare da murƙushe zanga-zangar masu adawa.
Museveni ya kuma faɗaɗa alaƙa da ƙasashe irin su China, Rasha, Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa domin rage dogaro da yammacin duniya.
Gano manyan rijiyoyin mai ya ƙara masa ƙarfi, inda aka cimma yarjejeniya da kamfanonin TotalEnergies da CNOOC don gina bututun fitar da mai.
A wannan zaɓe, babban abokin hamayyarsa shi ne Boni Wine, mawakin zamani mai shekaru 43, yayin da masana ke ganin ko da yake nasarar Museveni kusan tabbatacciya ce, batun gado da makomar mulki na ci gaba da tayar da ƙura, musamman dangane da rawar ɗansa Muhoozi Kainerugaba.
Reuters/NAN













































