Saudi Arabia ta haramta shiga da kaji da ƙwai daga Nijeriya, Afirka ta Kudu da wasu ƙasashe 38

poultry border

Hukumar kula da Abinci da Magunguna ta Saudi Arabia ta haramta shiga da kaji da ƙwai daga ƙasashe 40, tare da sanya takunkumi a wasu yankuna na ƙasashe 16, a matsayin matakin kariya ga lafiyar jama’a da kuma tabbatar da ingancin abinci a kasuwannin cikin gida.

Hukumar ta ce jerin ƙasashen da abin ya shafa na duba ne akai-akai bisa la’akari da sauye-sauyen halin kiwon lafiya a duniya da rahotannin bullar cututtuka.

Sabon jerin ya nuna cewa wasu daga cikin takunkumin sun fara aiki tun 2004, yayin da wasu aka ƙara su a hankali cikin shekaru, bisa tantance haɗari da kuma rahotannin ƙasa da ƙasa kan cututtukan dabbobi, musamman barkewar murar tsuntsaye mai tsanani.

Ƙasashen da aka sanyawa cikakken takunkumi a kansu sun haɗa da Afghanistan, Azerbaijan, Jamus, Indonesia, Iran, Bosnia da Herzegovina, Bulgaria, Bangladesh, Taiwan, Djibouti, Afirka ta Kudu, China, Iraq, Ghana, Falasdinu, Vietnam, Cambodia, Kazakhstan.

Sauran su ne, Kamaru, Koriya ta Kudu, Koriya ta Arewa, Laos, Libya, Myanmar, Birtaniya, Masar, Mexico, Mongolia, Nepal, Nijar, Najeriya, Indiya, Hong Kong, Japan, Burkina Faso, Sudan, Serbia, Slovenia, Côte d’Ivoire da Montenegro.

An kuma sanya takunkumi a wasu jihohi ko birane a Australia, Amurka, Italiya, Belgium, Bhutan, Poland, Togo, Denmark, Romania, Zimbabwe, Faransa, Philippines, Canada, Malaysia, Austria da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Hukumar ta bayyana cewa wannan haramcin na wucin gadi bai shafi naman kajin da aka sarrafa da zafi da sauran kayayyakin da suka danganci haka ba, matuƙar sun cika ƙa’idojin lafiya da tsaro da aka amince da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here