Shugaban jam’iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha ya yi kira ga Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulkin jihar, ko kuma a tsige shi.
Okocha ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ƴanmajalisar jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi.
Tun da fari, bayan hukuncin kotun ƙolin, majalisar jihar ta ba gwamnan jihar wa’adin kwana biyu ya sake gabatar da kasafin kuɗi, gayyatar da ya ƙi amsawa.
Karanta: El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma SDP
Daga baya shi kuma ya gayyace su gidan gwamnati domin su tattauna, inda su ma suka ce ba za su je ba, domin a kafofin sadarwa suka ga gayyatar.