A ranar Talata ne wata babbar kotun jihar Kano ta bayyana cewa manoma 238 a Katarkawa dake karamar hukumar Warawa a jihar Kano su ne ke da hakkin mallakar wani fili.
Karar da Alhaji Adamu Mohammad ya shigar a madadin manoman Katarkawa 237 sun nemi kotu ta ayyana su a matsayin masu filin mai fadin hekta 1,014 da ke Katarkawa a karamar hukumar Warawa.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an shigar da karar ne a shekarar 2016.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Lawan Wada-Mahmoud, ya bayar da umarnin cewa manoman 238 za su mallaki filin na tsawon shekaru 99.
Alkalin kotun ya ce wadanda suka shigar da kara sun tabbatar da da’awar da suka yi cikin bayanan da suka bawa kotun.
“Karmar Hukumar Warawa ba ta da ikon kwato fili bayan ta mika wa Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Kasa (NALDA) a karkashin Ma’aikatar Gona ta Tarayya.
“Da wannan hukuncin, ya kamata karamar hukumar Warawa ta daina kutsawa tare da ware kadada 1,014 da aka ware wa manoma.
“Wasikun rabon da aka bai wa manoman har yanzu suna nan kuma suna kan doka,” in ji alkalin.
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Mista Abba Shu’aibu, ya roki kotun da ta bayyana cewa wadanda yake karewa na da hakkin mallakar gonakinsu cikin lumana da kwanciyar hankali a Katarkawa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar sun gabatar da shaidu biyar da kuma baje koli 102.
Lauyan wadanda ake kara, Mista Murtala Shehu, ya gabatar da shaidu biyar da baje koli guda hudu.












































