Nijar ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu da su ringa bin ka’ida

Janar, Mohamed Boubacar Toumba, Nijar, gargadi, kungiyoyi, ka'ida
A jamhuriyar Nijar hukumomin mulkin sojin kasar sun yi kashedi dangane da yadda suka ce kungiyoyi masu zaman kansu na gida da na ketare masu aiki a Nijar...

A jamhuriyar Nijar hukumomin mulkin sojin kasar sun yi kashedi dangane da yadda suka ce kungiyoyi masu zaman kansu na gida da na ketare masu aiki a Nijar mafi akasarinsu na aiki ba tare da kiyaye dokokin kasa ba.

Ministan cikin gidan Nijar, Janar Mohamed Boubacar Toumba wanda ya yi kashedin yayin wani taron manema labarai ya kuma bayyana damuwa kan yaduwar kungiyoyi masu zaman kansu barkatai fiye da 3000 a kasar.

Karin labari: Ana binciken dalilin yawan tashin gobara a jihar Kano

Ya kara da cewa kungiyoyin na aiki ba tare da bayar da haske kan hanyoyin samar da kudaden shigarsu ba da yadda suke kashe su.

Ma’aikatar cikin gidan ta yi barazanar dakatar da kungiyoyin da ba su kiyaye dokokin aikinsu da dokokin kasa da ma sanar da yiwuwar dakatar da su da ma kama mambobinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here