Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta cafke wasu ’yan Najeriya biyu da suka dawo daga Brazil da suka hadiye hodar iblis da koken, inda suka fitar da jimillar rukunai 116 na miyagun kwayoyin a hannun jami’an hukumar a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Ikeja, Legas.
Wata sanarwa daga Daraktan yada labarai na NDLEA, Mista Femi Babafemi, ta bayyana cewa an kama mutum na farko mai suna Ofoma Sunday, mai shekaru 46, a ranar Talata 16 ga Satumba bayan ya iso daga Brazil ta jirgin Ethiopian Airlines, wanda aka yi masa gwajin hoton jiki wanda ya tabbatar da cewa ya hadiye kwayoyi.
Daga baya ya fitar da rukunai 111 na hodar iblis masu nauyin kilo 1.452 a wani otal da ake sa ran zai kai kayan.
Haka kuma, wani mutum mai suna Nweke Jude Chuckwudi, wanda aka tura domin karɓar kwayoyin, shi ma ya shiga hannu.
Hakazalika, an cafke wani mai suna Ukachukwu Frank Ikechukwu a filin jirgin saman Legas a ranar 19 ga Satumba bayan dawowarsa daga Brazil ta hanyar Addis Ababa. Gwajin jiki ya nuna ya sa miyagun kwayoyi a jikinsa.
Daga baya ya fitar da rukunai biyar na koka’in masu nauyin gram 145.
Ya shaida cewa ya sayi rukunai tara a Brazil ya sa a duburarsa, amma saboda zafi da rashin natsuwa ya zubar da biyu a birnin Addis Ababa, sannan daga baya ya rasa wasu biyu a cikin jirgi.
Ukachukwu ya kara bayyana cewa kafin wannan tafiyar yana harkar sayar da kaya ne a Brazil tun daga 2017.
Sai dai a shekarar 2020 ya tafi Amurka, inda aka kama shi da laifin shige da fice har aka tsare shi fiye da shekara guda kafin a kora shi zuwa Najeriya a 2022.
Shugaban hukumar NDLEA, Manjo Janar Mohammed Buba Marwa (rtd), ya yaba da aikin jarumtar jami’an da suka gudanar da wannan samame a Legas da wasu jihohi.
Ya bukace su da su ci gaba da yin aiki da jajircewa domin dakile safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar.













































