Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan matakin gaggawa na korar wasu mukarrabansa guda biyu sakamakon barazanar kisa da suakai wa alkalan kotunan dake sauraron kararrakin zaben gwamnoni.
Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan kasa da tsare-tsare, Adamu Aliyu Kibiya a ranar Alhamis a wani taron addu’a na musamman da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka gudanar ya zanta da ‘yan jarida, inda ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da cewa duk wanda a cikinsu ya karbi cin hanci don murde hukuncin. zai biya da rayuwarsa.
Har ila yau, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye, a wani faifan bidiyo a ranar Alhamis yayin taron addu’o’i na musamman da NNPP ta gudanar ya bayyana kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa, Khasim Shettima kan batun.
Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban NBA reshen Kano, Barr. Suleiman Gezawa a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da SOLACEBASE a ranar Juma’a ya bukaci gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da ya sanyawa kwamishinan takunkumi domin ya nuna cewa wannan magana ba ita ce matsayin gwamnatin jihar ba.













































