Matsalar Tsaro: Gwamnatin Kwara ta rufe Kwalejin Ilimi ta Oro

Kwara State College of Education

Gwamnatin Jihar Kwara ta ba da umarnin rufe Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ke Oro nan take, sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a yankin.
Umarnin ya fito ne a cikin wata takardar cikin gida mai kwanan wata 20 ga Janairu, mai lambar MOTE/CE/VOL.II/227, wadda Ma’aikatar Ilimin Manyan Makarantu, Kimiyya da Fasaha ta fitar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito.
Takardar, wadda Kwamishinar Ilimin Manyan Makarantu, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta sanya wa hannu, ta umurci shugabancin kwalejin da su rufe makarantar nan take, bisa umarnin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
A cewar takardar, an ɗauki matakin ne sakamakon ƙara ta’azzarar barazanar tsaro a kewayen makarantar, kuma yana daga cikin umarnin gwamnati na rufe dukkan makarantu a ƙaramar hukumar da abin ya shafa.
Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar ma’aikata, ɗalibai da al’ummar yankin, tana mai jaddada cewa tsaro shi ne ginshiƙin duk wani ci gaba.
Takardar ta ƙara da cewa rufe makarantar zai ci gaba da kasancewa har sai an kammala cikakken bitar tsaro, tare da umarnin a miƙa rahoton aiwatar da wannan umarni ga ma’aikatar ba tare da ɓata lokaci ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here