Malaman addinai ku guji yaudarar mabiyan ku – Sarkin Musulmi

Sarkin, Musulmi, ayyana, ranar, Lahadi, sabuwar, shekarar, Musulunci
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Lahadi 7 ga watan Yuli, 2024, a matsayin...

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gargadi malaman addini da su guji yaudarar mabiyansu domin cimma wata bukata ta su ta kanshin kai.

Ya umarce su da su tuba, su bi ingantacciyar koyarwar addininsu na gina al’umma ta gari.

Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya bayyana haka ne a wajen taron yakin Arewa kan matsalolin da suke damun Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar ranar Litinin a Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ofishin kula da addinai na jihar Kaduna tare da hadin gwiwar International Alert ne suka shirya taron.
“Bari in shawarci shugabannin addini da su guji yaudarar mabiyansu don amfanin kansu, galibin masu ibada a Masallatai da Coci suna kallon su a matsayin jagororin ruhi kuma suna dogara da su sosai.
“Ka yi iyakar kokarinka ka bauta wa Allah, ka bar maSa komai. An samu kalubale da dama a kasar nan, amma mun yi imanin cewa komawa ga Allah da yawaita addu’o’i a wuraren ibada zai kawo mafuta.”

“Masu wahala na ɗan lokaci ne, kuma babu abin da ke dawwama har abada. Mu ci gaba da yi wa shugabanninmu addu’a, mu guji yin Allah wadai, muna da imanin cewa Allah zai magance lamarin a matsayinsa na masani kuma mai gani.” Inji shi.

Sarkin ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanninsu, maimakon haka, su damka su ga hukuncin Allah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here