Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da Dan Majalisa

Hassan Umar, majalisar dokokin, jihar, kebbi, dakatar, dan majalisa
Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi ta Arewa, Hassan Umar, bisa zargin rashin tsaro. Hakan na kunshe...

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi ta Arewa, Hassan Umar, bisa zargin rashin tsaro.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardar majalisar, Suleiman Shamaki ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Karin labari: Dalilin da yasa ‘yan Sanda suka kama Aisha Galadima

Sanarwar ta kara da cewa dakatarwar ta biyo bayan wasu kalamai marasa tsaro da kuma tunzura wasu ‘yan majalisar kan shugabannin majalisar.

Ya kara da cewa, “Ni Suleiman Shamaki, magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, an umarce ni da na sanar da jama’a cewa Majalisar a zamanta na zartaswa da ya gudana a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, 2024.

Karin labari: Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Da Shirin Dashen Bishiyoyi Miliyan Uku A Kano

A don haka ta yanke shawara baki daya tare da dakatar da Hassan Umar, dan majalisar wakilai a Mazabar Birnin Kebbi ta Arewa, sakamakon kalamansa na rashin tsaro.”

Sannan ta lissafo sauran laifuffukan dan majalisar da suka hada da, “Turawa wasu ‘yan majalisar adawa da shugabancin majalisar da haifar da rashin jituwa tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa a majalisar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here