Majalisar Dattawa ta fara tantance Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC)

Joash Ojo Amupitan 750x430 (1)

Majalisar dattawa ta fara tantance farfesa Joash Ojo Amupitan, wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya zaɓa domin zama sabon shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), a zaman da aka gudanar a ranar Alhamis da rana a zauren majalisar.

Amupitan ya isa majalisar tare da gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’an gwamnati, inda ya fara karanta tarihin aikinsa a gaban ‘yan majalisar kafin su yanke hukunci kan tabbatar da shi ko akasin haka.

An shigar da shi cikin babban zauren majalisar dattawa ta hannun mai taimakon shugaban ƙasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Abubakar Lado.

Bayan haka, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya tarbi Amupitan da iyalansa da sauran baki.

An fara aikin tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana bayan jawabin shugaban majalisar, wanda ya bayyana tsarin gudanar da zaman.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, shi ne ya fara tambayoyi da izinin shugaban majalisar, inda ya bukaci Amupitan ya bayyana hanyoyin da zai bi wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta zama cikakkiyar mai zaman kanta da adalci.

Ana sa ran zauren majalisar zai yanke hukunci nan gaba kan tabbatar da Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta lasa (INEC), wanda zai maye gurbin shugaban da ya gabata bayan kammala wa’adinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here