Karamar hukumar Ifelodun da ke Jihar Kwara ta sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a yankin Oro-Ago da ke cikin yankin hukumar.
Sanya dokar hana fitar a yankin Oro-Ago ya biyo bayan ci gaba da ayyukan soji da ake yi a yankin Karamar hukumar Ifelodun domin fatattakar ‘yan bindiga da ke buya a dazukan yankin.
Shugaban karamar hukumar, Honorabul Femi Yusuf, ne ya sanar da sanya dokar hana fitar a yankin Oro-Ago ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta samu sa hannun sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar, Abdulquadri Jimba.
Sanarwar ta bayyana cewa dokar hana fitar ta fara aiki daga karfe 6:00 na safe a ranar Laraba, 28 ga Janairu, 2026, a matsayin wani bangare na hadin gwiwar matakan tsaro da aka dauka domin tarwatsa ‘yan ta’adda da ake zargi tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.
Ta kara da cewa a lokacin da dokar ke aiki, an haramta duk wani motsi na mutane da ababen hawa a fadin yankin baki daya domin bai wa jami’an tsaro damar ci gaba da aikin kawar da barazana da suke gudanarwa.
Sanarwar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa za a rika sanar da su duk wani sabon mataki ko sauyi game da matakan tsaro yayin da al’amura ke ci gaba da gudana.













































