Baki ɗaya kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa sun shiga ganawar sirri yanzu haka a Hedkwatar INEC da ke babban birnin tarayya Abuja.
Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan hukumar zaɓe ta umarci kwamishinanta na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, ya nesanta kansa daga harkokin hukumar da zaɓen Adamawa.
A ranar Lahadin da ta gabata, kwamishinan (REC) ya ta da ƙura da misalin ƙarfe 9:00 na safe lokacin da ya ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamna.
Channels tv ta rahoto cewa ayyana Binani a matsayin wacce ta ci zaben Adamawa ya haddasa cece-kuce duba da gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, na PDP ne a kan gaba a yawan ƙuri’u.
Karin bayani na nan tafe…













































