Kotu ta dage sauraron shari’ar zargin daukar nauyin ta’addanci da ake yi wa Malami da ɗansa

Abubakar Malami 750x430

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, kan zargin daukar nauyin ta’addanci zuwa ranar 15 ga watan Afrilu.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kasa ta gurfanar da Malami da dansa Abdulaziz a gaban kotu ranar 3 ga watan Fabrairu kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tsaron ta zargi Malami da kin gurfanar da masu daukar nauyin ta’addanci a gaban kotu duk da cewa an tura masa fayil din shari’arsu zuwa ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya domin a gurfanar da su.

A ranar 27 ga watan Fabrairu, kotu ta bayar da belin Malami da dansa kan Naira Miliyan 200 kowannensu tare da sharadin gabatar da mutane biyu da za su tsaya musu a kan adadin kudin.

A ranar Talata da aka sake zaman kotun, wadanda ake kara sun halarci kotun yayin da shari’ar ta zo gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik.

Lauyan masu gabatar da kara, Akinlolu Kehinde, SAN, ya shaida wa kotun cewa kwanan nan ne aka ba shi umarnin karbar ragamar shari’ar.

Ya bayyana cewa yana bukatar karin lokaci domin tuntubar shaidu kafin a fara sauraron shari’ar.

Sai dai lauyan wadanda ake kara, Shuaibu Arua, bai yi adawa da bukatar dage sauraron shari’ar ba.

A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Abdulmalik ta amince da bukatar sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 da 16 ga watan Afrilu domin fara sauraro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here