Kamfanin samar da kayayyakin aikin gona na jihar Kano (KASCO), ya tabbatar da sahihancin rahoton binciken kuɗi da kafar yaɗa labarai ta SolaceBase ta wallafa, inda ya amince da cewa an samu kura-kurai da rashin daidaito a harkokin kuɗi da gudanarwa na kamfanin.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen gudanarwa da ayyuka na KASCO, Aminu Sadiq, ya fitar a daren ranar Alhamis, kamfanin ya ce, yawancin matsalolin da aka gano sun faru ne a shekarar 2019, a zamanin tsohuwar gwamnati, kuma ba su da alaƙa da shugabancin da ke kan mulki a yanzu.
Rahoton harkokin kuɗin, wanda ya duba bayanan kuɗin KASCO har zuwa ranar 31 ga Disamban 2024, ya gano ƙarancin bayyana adadin kuɗaɗen shiga, ƙara yawan riba na bogi, raunin tsarin kula da kuɗi, da rashin cikakken bayanan lissafi.
Daga cikin abin da aka gano, KASCO ya bayyana cewa kuɗaɗen juyin kasuwancinta sun kai naira biliyan 4.7, amma binciken ya nuna cewa ainihin adadin ya kai naira biliyan 5.3, lamarin da ya haifar da bambancin sama da naira biliyan 1.2.
Haka kuma, an samu rashin dai-daito a kudaden haɗa taki da ribar ajiya a banki.
Rahoton ya kuma nuna babban banbanci tsakanin littafin kuɗi da bayanan banki, inda aka gano gibin sama da naira biliyan 2, tare da ƙarancin bayyana kuɗaɗen sayen kayayyaki da albarkatun noma.
Bugu da ƙari, an gano kashe kuɗaɗen tafiye-tafiyen ƙasashen waje da darajar dala 50,630 ba tare da cikakkun bayanai ko amincewa ba.
Sai dai KASCO ya jaddada cewa tun bayan hawan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, an bayar da umarnin gudanar da cikakken binciken kuɗi na dukkan shekarun da ba a duba ba, inda aka tura dukkan matsalolin da aka gano zuwa Hukumar Karɓar Ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, kuma a halin yanzu suna gaban kotu, tana mai yabawa da yadda gwamnatin yanzu ke ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.












































