Jami’an Hukumar EFCC Mai yaki da masu yiwa tattalin Arzikin Kasa ta’annati sun yi wa Kasuwar Yan Chanji ta Wapa da ke karamar hukumar Fagge, a Jihar Kano dirar mikiya.
Jaridar Solacebase ta tawaito cewa a lokacin da jami’an hukumar suka isa kasuwar ta Wapa galibin ma’aikatan sun nemi mafaka yayin da wasu suka rufe shagunansu da fargabar kama su.
Rahotanni sun ce jami’an na EFCC na gudanar da bincike kan zargin da ake yi na cewa wasu mutane na yin sama-da-fadi tare da tara kudaden kasashen waje wanda hakan ke haifar da karanci da ke kara tashin farashin dala.
Sai dai ’yan kasuwar canjin sun yi mamakin yadda jami’an da suka zo cikin motocin bas guda uku suka ce kada su firgita domin ba wai sun zo su kama su ba ne, sai dai su wayar da kan su kan rage tabarbarewar canjin dala da ake yi zuwa Naira.
Yanzu haka dai Farashin canjin dalar Amurka da Naira na ci gaba da tashi, lamarin da ya jefa mutane cikin damuwa kwanaki kadan da suka gabata inda ake musayar Dala daya akan Naira 715.
Duk da cewa a cikin kwanaki biyun da suka gabata ana iya samun Dala 1 kan Naira 620 a Kano.
Wani jami’in canjin da ya zanta da Jaridar Solacebase, Ibrahim Sale Dahiru, ya ce da farko sun ji tsoron ko za a kama su ne lokacin da suka ga jami’an EFCC dauke da ‘yan sanda da makamai.
Sai dai kuma, sakataren kungiyar masu canji, Alhaji Sani Ilera Wapa, wanda shi ma ya tabbatar da zuwan jami’an cikin kasuwar ya ce babu wanda aka kama yayin atisayen.
Ya ce ‘yan sandan sun zagaya kasuwar amma basu ce komai ba game da aikinsu ba.

Jaridar Solacebase ta yi kokarin tattaunawa da EFCC a Kano sai dai basu samu lambar Mai magana da yawun hukumar ta EFCC ba.













































