INEC Ta Fitar da Cikakkun Bayanan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa, da majalisun tarayya

INEC Mahmood
INEC Mahmood

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta wallafa bayanan wasu ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka tsayar a zaben 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa hukumar INEC ta wallafa wannan labari ne ranar Juma’a a ofisoshinta da ke birnin tarayya Abuja.

Bayanan sun hada da na ‘yan takarar shugabancin kasa da mataimakansu da kuma ‘yan takarar majalisar dattawa da na wakilai.

Bayanan sun hada da na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa, Mista Ibrahim Masari.

Haka kuma ta wallafa bayanan Abiola Kolawole, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP da abokin takararsa, Ribi Marshal sai Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP da abokin takararsa, Johnson Oladipupo.

Sauran sun hada da Yabagi Sani, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADP da abokin takararsa, Udo Okey –Okoro sai Ado-Ibrahim Abdulmalik, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar YPP da abokin takararsa, Enyinna Kasarachi.

Kazalika, akwai Omoyele Sowere, dan takarar shugaban kasa na AAC da abokin takararsa, Garba Magashi da Mamman Dantalle, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM da abokin takararsa Ojei Princess.

Hukumar ta INEC ta kuma wallafa bayanan Chukwudi Umeadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APGA da abokin takararsa Koli Mohammed, da Oluwafemi Adenuga, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar BP da abokin takararsa Turaku Mustapha.

Sauran sun hada Daberechukwu Nwanyanwu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da abokin takararsa, Ramalan Abubakar da kuma Dumebi Kachikwu dan takarar shugaban kasa, jam’iyyar ADC da abokin takararsa, Ahmed Mani.

Sai kuma Hamza Almustafa, dan takarar shugaban kasa, na jam’iyyar Action Aliance (AA) da abokin takararsa Chukwuka Johnson da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here