Gwamnatin tarayya ta fara aikin gina titin Jakara – Wuju – Wuju da kuma aikin magudanan ruwa na Naira biliyan 47 a cikin birnin Kano.
Aikin yana daga cikin manyan ayyukan more rayuwa da ake sa ran za su inganta zirga-zirga da tsaftar muhalli a yankin.
Aikin titin zai ratsa ƙananan hukumomin Gwale, Karamar Hukumar Birni, Dala da Fagge a jihar Kano.
An tsara shi ne domin dakile matsalar zaizayar ƙasa tare da ƙarfafa harkokin tattalin arziki a yankunan da titin zai ratsa bayan kammalawa.
Ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane na tarayya, Alhaji Yusuf Ata, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta karɓi aikin ne bisa buƙatar gwamnatin jihar Kano.
Karanta: Mijina ya yarda da jita-jitar Aso Rock cewa na shirya kashe shi – Aisha Buhari
Ya ce wannan mataki na nuni da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen aiwatar da muhimman ayyuka.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kano ta riga ta kammala aikin titin mai tsawon mita 850 kafin gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin ci gaba da gina sauran kilomita 6.7 da suka rage.
Ya bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen hanzarta kammala aikin cikin lokaci.
Ya kuma ce gwamnatin jihar Kano ce za ta ɗauki nauyin biyan diyya ga kadarorin da aikin ya shafa.
Wannan, a cewarsa, zai ba da damar aiwatar da aikin ba tare da tsaiko ba.
Alhaji Yusuf Ata ya yaba wa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso bisa ƙaddamar da aikin tun shekarar 2013, sannan ya gode wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa amincewa da kuɗaɗen aiwatar da aikin.
NAN













































