Gwamnatin jihar Kano tayi mana rinton aiki – APC 

Ganduje, Tinubu, APC, Kano, Gwamnati
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa wanda mazaɓarsa ta ce ta dakatar da shi, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa...

Jam’iyyar Apc a karamar hukumar Kiru ta zargi gwamnatin jihar Kano da yin riton aikin asibiti na garin Kafin Maiyaki, inda tace asibitin Ganduje ne ya gina ba Abba.

Bayanin haka na kunshe cikin wata sanarwa da Shugabancin Jam’iyyar Apc na Karamar Hukumar Kiru, Aminu Alhassan Kiru, ya fitar a ranar Juma’a.

” A madadin kafatanin ‘yan Jam’iyyar muna sanar da duniya cewa labarin da ake yadawa cewar gwamnatin Nnpp ta Jihar Kano ta gina da samar da kayan aikin asibiti a garin Kafin Maiyaki ba gaskiya bane, rinton aiki ne da suka saba.”

“Wannan asibiti na garin Kafin Maiyaki, gwamnatin Apc karkashin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ce ta gina shi a zamaninsa tare da samar da dukkan kayayyakin da yake bukata don samar da ingantaccen kulawa ga al’ummar wannan yanki.”

“Muna janyo hankalin al’ummar wannan Jiha da suyi watsi da wannan farfaganda ta rinton aiki da jami’an gwamnatin Nnpp suka fitar akan samar da wannan asibiti musamman saboda hujjojin da zamu gabatar a wannan rubutu.”

“Bayan ayyukan gini da gwamnatin Jihar Kano ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta samar, akwai dakin kwanciya sabo wanda tsohon danmajalisar tarayya na Apc Hon. Aliyu Datti Yako ya gina a wannan asibiti tsakanin 2019 – 2023 kamar yadda ake iya gani a cikin hotunan.”

“Wannan aikin gini an fara shine a zangon farko na gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje (2015 – 2019) wanda aka baiwa kamfani mai suna Maiyaki Integrated
Links Limited.”

“Bayan kammala aikin ginin da gwamnatin tayi, an sake baiwa kamfanin Maiyaki Integrated Links Limited kwangilar sayo kayayyakin amfani a wannan asibiti akan kudi N132, 763, 047:49 kamar yadda yake kunshe a takarda mai lamba MOH/SMTB/001/2020/I/23 ta ranar 7/1/2021 kamar yadda yake a rubuce a jikin takardar dake hade da wannan rubutun.”

“Domin sake tabbatar da karyar da sukayi, mun tanadi hotuna na bikin karbar kayan asibitin da akayi ranar 24/5/2023 da kuma bikin kaddamar da kayan asibitin da aka kawo wanda Shugaban Karamar Hukumar Kiru ya jagoranta ranar 27/5/2023 wanda har Maigirma Hakimin Kiru, Danmadamin Karaye ya halacci wajen wannan taro.”

“Dangane da wadannan hujjoji da muka gabatar, muna janyo hankalin mutanen wannan jiha da suyi watsi da wannan farfaganda da gwamnatin Jiha ta Nnpp take yadawa cewa ita ta samar da wannan asibiti da kayan aiki a garin Kafin Maiyaki kuma muna basu shawara akan su daina rinton ayyukan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi su tsaya su daina kirkirar rigingimun siyasa da yake hanasu nutsuwa suka kasa yiwa al’ummar Jihar Kano ayyukan raya kasa.”

“Mu al’ummar wannan karamar hukuma ta Kiru ba timawa bane, munsan wanda yayi mana aiki kuma tuntuni mun riga munyi masa godiya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here