Gwamnatin jigawa ta kaddamar da Kwamitoci dan samar tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa

flood in yobe
flood in yobe

Gwamnatin jigawa ta kaddamar da Kwamitoci dan samar tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa

Gwamnatin jihar Jigawa a ranar talatar nan ta kaddamar da wasu kwamitoci guda biyu domin dakile illolin ambaliyar ruwa a jihar.

Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne ya kaddamar da kwamitocin a gidan gwamnati dake Dutse.

Idan dai za a iya tunawa, sama da mutane 133 ne suka rasa rayukansu da dukiyoyin masu tarin yawa sakamakon ambaliyar ruwan.

Badaru ya ce kwamitocin biyu sun hada da, kwamitin tantance bala’in ambaliyar ruwa na jiha, da tara kudade, da kuma kwamitin kwararru kan dakile barazanar ambaliyar ruwa.

A cewarsa, “An dorawa kwamitin bayar da tallafin alhakin tattara tallafi da raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin jihar.

Izuwa yanzu gwamnatin jihar ta karbi sama da naira milyan 500 na ​​tallafin kayayyakin agajin ambaliyar ruwa daga gwamnatin tarayya, masu hannu da shuni, da daidaikun mutane.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here