Gwamnati ta soma biyan malaman jami’a kudaden ariyas

ASUU ASUU NEW 660x381 1
ASUU ASUU NEW 660x381 1

Gwamnatin tarayya ta soma biyan kudaden ariyas ga malaman jami’a da kuma malaman kwalejojin kimiya da fasaha na kasar nan.

Shugaban kungiyar Malaman kwalejojin kimiya da fasaha na kasa Dakta Anderson Ezeibe, ya tabbatar da haka ga jaridar Punch.

Ya ce wasu daga cikin mambobin su sun fara jin alat na ariyas din amma kuma albashi har yanzu shiru.

Shima shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar fasaha dake Minna a Jihar Neja Dakta Gbolahan Bolarin ya ce wannan somin tabi ne gwamnatin tarayya ta ta yi musu.

A wani Labarin kuma mahukuntan jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola ta ce za ta koma harkokin karatu daga ranar alhamis 26 ga watan da muke ciki na Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here