Gwamnan Sokoto ya amince da fara biyan alawus ga limamai kowanne wata

Ahmed Aliyu 750x430

Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da fara biyan limamai da mataimakansu da kuma masu kiran sallah a fadin jihar alawus-alawus na wata-wata tare da sabon Kasafi ga Masallatan Juma’a.

A wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gidan gwamnati Abubakar Bawa ya fitar ranar Asabar, ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na karfafa yaɗa addinin musulunci da inganta haddar kur’ani a tsakanin yara.

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ne ya sanar da daukar matakan a yayin bikin yaye malaman haddar Alkur’ani 111 na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi reshen Sokoto.

Gwamna Aliyu ya bayyana cewa an ba su alawus-alawus da kuma rabon masallatai ne da nufin tallafa wa malamai don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata tare da tabbatar da cewa koyarwar addinin Musulunci ta ci gaba da bunkasa a jihar.

“Mun kuma gabatar da ƙayyade kudade na wata-wata ga dukkan masallatan Juma’ar mu, daga N300,000 zuwa N500,000 ya danganta da nau’insu.

“Bugu da kari, an gabatar da alawus-alawus na wata-wata ga Limamai, mataimakansu, da masu kiran sallah a fadin jihar don tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu,” inji shi.

Gwamnan ya tabbatar da cewa al’amuran addinin musulunci sun kasance abin fifiko a tsarin gwamnatinsa wanda ke matsayi na biyu bayan tsaro.

Tinubu Ya Aike Da Ta’aziyyarsa Ga Iyalai Da Mabiya Na Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu

Ya kuma umurci mahukuntan makarantar da su gano filayen da za a kafa wurin zama na dindindin, inda ya ba da tabbacin gwamnatin jihar za ta bayar da tallafin da ya dace.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya yabawa Sheikh Dahiru Bauchi bisa kafa gidauniyar, ya kuma yabawa malamai a jihar kan yadda suke inganta manufofin addinin musulunci da zaman lafiya.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko wanda ya samu wakilcin Aminu Sufi, ya bukaci iyaye da su karfafa ‘ya’yansu wajen rungumar haddar Alkur’ani.

Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, wanda Lawal Liman ya wakilta, ya yi alkawarin ci gaba da baiwa gidauniyar tallafin naira miliyan 22 tare da tallafin kayan abinci ga daliban da aka yaye da kuma makarantar.

A nasa jawabin Sheikh Bauchi, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana cewa, fadada wannan gidauniyar zuwa wasu jahohi, an yi shi ne don sanya yara su tsunduma cikin tsarin karatun Alkur’ani da kuma dakile barace-barace a kan tituna.

Kowanne daga cikin dalibai 111 da aka yaye ya samu kudi naira 20,000 da kayan sawa daga gwamnatin jihar Sokoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here