Gwamnan Kano ya umarci dukkan kwamishinonin da ya zaɓa su bayyana abinda suka mallaka

IMG 20230618 WA0183
IMG 20230618 WA0183

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan kwamishinonin da ya zaɓa su bayyana abinda suka mallaka.

Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya ce wajibi ne kowane kwamishina ya cike fam ɗin bayyana dukiya ko kuma ya rasa muƙamin.

Abba ya lashi takobin cewa ba zai rantsar da kowaye ya kaucewa Fam ɗin bayyana dukiya ba.

Ya ce gwamnatinsa zata tabbatar da gaskiya da haƙƙin sauke nauyi domin yin adalci da jagoranci na gari.

Karin bayani yanan tafe…..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here