“Gazawa ce APC ta fito tana zargin ‘ƴan adawa” – Jam’iyyun Adawa

Jam'iyyun, adawa, APC, PDP, LP, gazawa, zargin
Jam'iyyun adawar Najeriya sun mayar wa APC mai mulki martani, kan zarginsu da hannu wajen tunzura jama'a domin yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bore...

Jam’iyyun adawar Najeriya sun mayar wa APC mai mulki martani, kan zarginsu da hannu wajen tunzura jama’a domin yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bore.

Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kano, da Neja da Legas, kan tsadar rayuwa.

Sai dai a cewar jam’iyyun adawar APC ce a kan mulki, don haka alhakin tabarbarewar lamurra a kasar ya rataya ne a wuyanta.

Karanta wannan: Shugaba Tinubu ya koka kan karin farashin kayan abinci

Manyan jam’iyyun adawar Najeriya PDP da LP, sun ce kunar rigar jam’iyyar APC ce ke neman kayar da ita, kuma tun farko kankanba ce ta kai ta ga neman sahalewar ‘yan Najeriya domin jagorantarsu, ba tare da wani tartibin tsarin yaye musu matsalolin da suke ciki ba.

Shiyasa a yanzu bayan shafe kusan shekara guda a kan Mulki da shugaba Tinubu ya yi, take zarginsu da yi wa gwamnati shune, kamar yadda jam’iyyun biyu suka bayyana.

Mataimakin kakakin babbar jam’iyyar adawar PDP na kasa Malam Ibahim Abdullahi, ya ce ” APC ta sauka ta ba su mulkinta, domin tana zuga da tunzura al’umma idan tana ganin hakan shi ne daidai.”

Karanta wannan: Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa Auwal Shu’aibu Aranposu ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.

“Talaka na ciki halin ha’ula’i na mummunan rashin tsaro, da ƙangi na talauci da ƙunci na rashin inda zai saka gaba, amma a ce bai da ikon ya fito ya faɗi halin da yake ciki, sai gwamnati ta zargi jam’iyyun adawa, wannan rainin wayau ne a dake ka kuma a hanaka kuka,” in ji Malam Ibrahim.

A cewarsa “Kowa a Najeriya ya san halin da ake ciki, a gwamnatance APC ta gaza-gaza, ba su iya ba.”

Irin wannan martani ne ita ma jam’iyyar adawa ta LP ta mayar, tana mai nuni da cewa kamata ya yi APC ta zargi kanta, ba wai zargin ‘ƴan adawa ba.

Karanta wannan: ‘Yan bindiga sun kashe manoma uku tare da sace wasu da dama a Birnin Gwari

Kakakin jam’iyar LP na ƙasa Dakta Tanko Yunusa ya ce “Su ne da kan su suka tunzura mutane saboda sun yi wa al’umma ƙwace, sun saka su cikin yunwa, sannan an hana su magana, kun hana su zuwa makarantu, kun ce kada su je gona saboda riƙon sakainar kashi da suka yi wa mutane.”

Dakta Tanko ya ce da gwamnati ta yi abin da ya dace da ba’a samu matsalar da ake fuskanta ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here