Gasar NPFL: Ƙungiyar Barau FC ta naɗa Rabi’u Tata a matsayin kocin ta na riƙon ƙwarya

Barau FC Rabiu Tata

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta naɗa Rabi’u Tata a matsayin mai ba da shawarar fasaha na riko bayan kocin ƙungiyar, Ladan Bosso, ya sauka daga mukaminsa domin kula da lamuran iyalinsa.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na Barau FC, Ahmad Gwale, ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Ya ce Tata, wanda tsohon mataimakin koci ne a ƙungiyar, zai jagoranci shirye-shiryen fasaha da dabaru na ƙungiyar kafin wasan Gasar Firimiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NPFL) na zagaye na tara da za su fafata da ƙungiyar Kano Pillars a ranar Lahadi mai zuwa.

Sanarwar ta nuna cewa shugabancin Barau FC ya amince da naɗin Rabi’u Tata a matsayin mai ba da shawarar fasaha na wucin gadi da gaggawa, sakamakon janyewar Ladan Bosso saboda dalilai na iyali.

Ƙungiyar ta nuna godiya ga Bosso bisa ƙwarewa da sadaukarwarsa wajen ci gaban Barau FC tun lokacin da ya karɓi jagoranci a farkon kakar wasa.

An kuma bayyana cewa Tata zai yi aiki tare da sauran ma’aikatan fasaha don tabbatar da ci gaba da daidaiton ƙungiyar a cikin gasar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Barau FC tana matsayi na 19 a jadawalin Gasar Firimiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NPFL), kuma za ta buga wasa da Kano Pillars a karshen mako a wasa mai cike da ƙalubale na yankin Arewa maso Yamma.

Masoya da magoya bayan ƙungiyar sun nuna kwarin gwiwa cewa shugabancin Tata zai farfaɗo da ƙungiyar tare da dawo da kwarin gwiwa da kwazo a cikin wannan lokaci na rikon kwarya.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here