EFCC ta gurfanar da manyan ma’aikatan hukumar NRC uku kan zargin badaƙalar Naira biliyan 2.04

pixlr 20260225182407243

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da manyan jami’ai uku na Hukumar Kula da Layin Dogo na Kasa (NRC) a gaban Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja kan zargin almundahana da wankiyar kudade.

Wadanda ake tuhuma sun hada da Felix Njoku, tsohon Daraktan Kudi na NRC; Benjamin Chinwuba Iloanusi, Darakta a sashen saye da sayarwa na NRC; da Oche Jerry Ogbole-Inalegwu, Daraktan sashen injiniya (Mechanical).

An gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume daban-daban da suka shafi zargin cin amanar ofis, wankiyar kudade da kuma karbar kudade ba bisa ka’ida ba da suka kai sama da Naira Biliyan 2.04.

An gurfanar da Njoku a gaban Mai Shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ta Kotun Musamman kan Laifuffuka a Ikeja bisa tuhume-tuhume guda 17 da suka shafi zargin damfarar Naira 736,320,807.08.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce Njoku, bayan ya bar mukaminsa na Daraktan Kudi na NRC, tsakanin 2 ga Janairu zuwa 3 ga Disamba, 2024, ya karbi Naira 240,940,000 daga ‘yan kwangilar NRC ta asusun kamfaninsa na FC Njoku and Company da ke Zenith Bank, bisa alaka da kwangilolin da aka bayar a lokacin da yake kan mukami.

Shi kuma Iloanusi an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Ismail Ijelu na Babbar Kotun Jihar Legas kan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin damfarar Naira 915,265,472.60.

Ana zarginsa da karbar Naira 160,930,458.04 daga ‘yan kwangilar NRC ta asusun bankinsa na bankin Polaris tsakanin 4 ga Janairu zuwa 30 ga Disamba, 2022, lokacin da yake Daraktan sashen saye da sayarwa, bisa kwangilolin da aka bayar yayin gudanar da aikinsa.

Ogbole-Inalegwu kuwa an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Mojisola Dada ta Kotun Musamman kan Laifuffuka a Ikeja kan tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin damfarar Naira 395,190,600.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce yayin da yake Manajan Yankin Layin Dogon Kasa, kuma yana hulda da sunan Altech Engineering Services, ya karbi Naira 11,397,500 daga kamfanin China Civil Engineering Construction Company (CCECC) tsakanin 12 ga Fabrairu zuwa 29 ga Oktoba, 2019.

Ana ci gaba da sauraron karar a kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here