Wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan ayarin motocin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda na shiyya ta 12 da hedikwatarsa ta ke Bauchi, Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa.
Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, an gano cewa AIG din na kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi wa motarsa kwanton bauna.
lamarin ya faru ne a tsakanin Barde da Jagindi a jihar Kaduna a ranar Talata da misalin karfe 2:30 na rana.
AIG din yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba yayin da aka tsaurara matakan tsaro a kewayen shiyyar. Wata majiyar kuma ta bayyana cewa an tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa yankin domin fatattakar ‘yan ta’addan tare da tsaftace dajin.












































