Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya nada sabon sakataren rundunar na kasa da kasa

IGP, Kayode, Egbetokun, babban, sufeto, janar, 'yan sandan, najeriya, nada, sabon, sakataren, kasa da kasa, rundunar
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya amince da tura wasu manyan jami’an ‘yan sanda biyu zuwa manyan mukamai a cikin...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya amince da tura wasu manyan jami’an ‘yan sanda biyu zuwa manyan mukamai a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya a ci gaba da kokarin da ake yi na kara inganta aikin rundunar da hanyoyin magance miyagun laifuka a kasashen duniya daban-daban.

SolaceBase ta rawaito cewa an nada AIG Yetunde Longe a matsayin sakataren rundunar. A bisa wannan matsayi, AIG Longe ne zai dauki nauyin kula da ayyukan sakatariyar hedikwatar rundunar, da tabbatar da aiwatar da manufofi da umarnin IGP yadda ya kamata, da kuma daidaita harkokin manyan jami’an ‘yan sanda.

Karin labari: Buhari ya roƙi ‘yan Najeriya su sakawa gwamnatin Tinubu albarka

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, AIG Idowu Owohunwa an tura shi aiki a hukumar ta INTERPOL ta kasa (NCB) a sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Abuja.

An dora masa alhakin inganta hadin gwiwar ‘yan sandan kasa da kasa da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta cika hakkinta a cikin tsarin INTERPOL na duniya.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano ya umarci jami’an tsaro su kama masu zanga-zanga

Sufeto Janar na ‘yan sandan ya kuma yabawa manyan jami’an ‘yan sandan bisa kwazo da hidimar da suke yi wa rundunar ‘yan sandan Najeriya, ya jaddada cewa sabbin ayyukan da suka yi wata shaida ce ta kwarewa ta musamman da kuma amanar da rundunar ta ba su.

Abubuwan da aka buga suna nan da nan kuma suna bin ritayar magabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here