Babban bankin Ghana ya dakatar da lasisin GTB dana First-Bank

Babban Bankin, Ghana, dakatar, GTB, FBN, lasisi
Babban bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin musayar waje na GTB dana FBN saboda munanan ayyuka da suka hada da takardun zamba na wata guda...

Babban bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin musayar waje na GTB dana FBN saboda munanan ayyuka da suka hada da takardun zamba na wata guda.

Bankin Ghana, a cikin wata sanarwa da ya sanar da dakatarwar, ya ce “Bankin Ghana ya dakatar da lasisin ciniki na musayar waje na GTB Ghana Limited da FBNBank Ghana Limited, daga ranar 18 ga watan Maris na 2024, na wani lokaci.

Wata daya daidai da sashe na 11 (2) na dokar musanya waje ta 2006, (Dokar 723).

Karin labari: An sanya wa’adin rufe rajistar aikin Hajji a Kamaru

“Wannan ya samo asali ne sakamakon keta ka’idojin kasuwar canji daban-daban, ciki har da takardun bogi a ayyukansu na musayar kudaden kasashen waje da suka shiga hannun Bankin Ghana.

“Za’a maido da lasisin ne a karshen wa’adin dakatarwar na wata daya da zarar bankin Ghana ya gamsu da cewa sun samar da ingantattun tsare-tsare don tabbatar da bin ka’idojin kasuwar canjin kudade.

“Ta wannan bayanin, muna gargadin ‘yan kasuwar musayar kasashen waje da su bi ka’idoji na kasuwannin forex.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here