Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ba da rahoton satar waya sama da miliyan 25 tsakanin Maris 2023 da Afrilu 2024, sakamakon wani bincike da aka gudanar a 2024.
Rahoton na NBS mai suna Crime Experience and Security Perception Survey 2024, ya nuna cewa kimanin mutane 17,965,741 ne aka sace musu wayoyin su.
Satar waya, wanda laifi ne wanda ya zama ruwan dare a Najeriya.