Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da sabon jadawali da tsarin ayyuka na babban zaɓen 2027, inda ta sauya ranakun zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni domin dacewa da tanadin Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai kan Masu Zaɓe, Malam Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce sauyin ya biyo bayan soke Dokar Zaɓe ta 2022 da kuma kafa sabbin lokuta na doka a ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026.
Tun da farko, hukumar ta tsayar da ranar 20 ga Fabrairu, 2027 domin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, sai kuma 6 ga Maris, 2027 domin zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.
Karin karatu: Yanzu-yanzu: ADC da NNPP sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026
Sai dai a sabon jadawalin, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya ranar Asabar 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar Asabar 6 ga Fabrairu, 2027.
Hukumar ta kuma bayyana muhimman matakai kafin zaɓen, inda ta ce za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa daga 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, ciki har da warware rikice-rikicen da ka iya tasowa.
Kamfen ɗin ‘yan takarar shugaban ƙasa da na majalisun tarayya zai fara daga 19 ga Agusta, 2026, yayin da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi zai fara daga 9 ga Satumba, 2026.
INEC ta jaddada cewa kamfen dole ne ya tsaya awanni 24 kafin ranar zaɓe, tare da gargadin jam’iyyun siyasa da su bi jadawalin da doka ta tanada.
Haka kuma, hukumar ta sauya ranar zaɓen gwamnan Jihar Osun daga 8 ga Agusta zuwa 15 ga Agusta, 2026, tana mai cewa duk sauran matakan da suka rage za su bi sabon tsarin dokar.
Sauyin ranakun na zuwa ne kwanaki 13 bayan da hukumar ta fara sanar da ranakun zaɓen a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, lamarin da ya jawo suka daga wasu ‘yan ƙasa saboda ya yi daidai da watan Ramadan.
Sabon jadawalin ya zo ne kwanaki takwas bayan Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Zaɓe ta 2022 (Soke da Sake Kafawa) ta 2026 bayan amincewar Majalisar Tarayya.
Da wannan sabon jadawali, ana sa ran jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da masu zaɓe za su daidaita shirye-shiryensu gabanin babban zaɓen 2027.













































