Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta bayyana tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a matsayin mamba a Kwamitin yakin neman zaben ta.
Darakta-Janar na Kwamitin yakin neman jam’iyyar PDP Kuma gwamnan sokkoto Aminu Tambuwal, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce nadin Dogara “yana daga cikin ayyukan da muke ci gaba da yi na hada kai da dan takararmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, domin mu maido da babbar kasar mu Nijeriya”.
Idan dai ba a manta ba, Dogara ya jagoranci ayarin ‘ya’yan jam’iyyar APC na arewa wajen mubaya’a ga Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Dan majalisar wakilan mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na tarayya ya yi Allah wadai da tikitin mabiya APC na Bola Tinubu da Kashim Shettima.










































