Tsohon ministan wutar lantarki da karafa a jamhuriya ta biyu Paul Unongo ya rasu.
Unongo wanda ya fito daga gundumar Jato a karamar hukumar Kwande ta jihar Benue, ya rasu ne a babban birnin jihar Filato yana da shekaru 87 a duniya.
Wata majiya daga makusantan sa ta tabbatar wa manema labarai ta wayar tarho a ranar Talata a garin Makurdi.
Wata majiya a jihar da ba ta so a ambaci sunanta ba, ta tabbatar da rasuwarsa.
An haife shi ne a ranar 26 ga Satumba alif 1935, Paul Unongo, dan zuriyar Kwaghngise-Anure- Abera ne, a garin Turan, karamar hukumar Kwande ta jihar Benue.












































