Elon Musk ya yi tayin sayen kamfanin Twitter kan sama da Dala Biliyan 43

Elon Musk
Elon Musk

Shugaban kamfanin kera motoci na Tesla, Elon Musk, ya yi tayin sayen dandalin sada zumunta na Twitter kacokam kan zunzurutun kudi Dalar Amurka biliyan 43 da Dala miliyan 400, domin ya fito da wata baiwa ta musamman da kamfanin ke da ita.

Cikin wata sanarwa da ya fitar Elon Musk, ya ce zai biya dala 54 da doriya kan kowane hannun jari guda.

A baya bayan nan ne aka ruwaito cewa Elon Musk ya zama mutum mafi girman hannun jari a kamfanin na Twitter bayan ya kara yawan hannayen jarinsa.

Ya kara da cewa:
“Zan yi tunanin sauya matsayina na mutum mafi yawan hannun jari, a wannan kamfanin matukar ba a karbi tayin dana yi ba.” Inji Musk.

Wasu bayanai da ya mikawa hukumar kula da harkokin kudi ta Amurka sun nuna sakonnin da Musk ya turawa majalisar amintattu na Twitter cewa ya yanke shawara a karshen mako ya kamata kasuwancin kamfanin ya zama mai zaman kansa.

An gayyaci Mista Musk ya kasance cikin majalisar amintattun kamfanin amma Twitter a ranar Lahadi ya sanar da cewa ya janye tayin da ya yi masa.

Cikin bayanan, Musk ya ce ba ya son “jeka-ka-dawo” sannan ya ce: “Tayi ne mai tsoka kuma masu hannun jarinku za su so shi.”

Elon Musk, ya kara da cewa zai dauki matakin sayar da hannun jarinsa na Twitter idan har ba a karbi tayin nasa ba.

“Wannan ba barazana ba ce, kawai dai ba zai zama zuba jari kai waye ba idan ba a samu sauyin da ake bukata ba,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here