Ma’aikatan Max Air sun tsere yayin da fasinjoji suka yi zanga-zangar jinkirin tashin jirgi

Max Air protest 1
Max Air protest 1

Wasu fasinjojin jirgin Max Air sun yi dirar mikiya a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Laraba.

Lamarin wanda ya faru a sashen zirga-zirgar jiragen cikin gida na filin jirgin, ya haifar da hatsaniya yayin da fasinjojin suka zargi kamfanin da jinkirta tashin su na sa’o’i ba tare da bayar da wani dalili ba.

Wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sadarwa na zamani, ya nuna yadda fasinjojin ke huce haushinsu yayin da daya daga cikinsu ya lalata kayayyaki a kan titin jirgin.

Da yawa daga cikin fasinjojin sun kutsa kai cikin sashen kamfanin, inda suka lalata kayan aiki bayan da jami’ansu suka gudu.

Rahotonni sun bayyana cewa, fasinjojin da suka sayi tikitin jirgin zuwa Legas sun fusata bayan da kamfanin ya sanar da cewa an sake jadawalin tashin jirgin da safe.

“Sun ci gaba da sanar da sauya jadawalin jirgin tun da safe, Na zo nan tun ƙarfe 9:30 na safe kuma ƙarfe 6:30 na yamma ne, babu wanda ya ce mana komai,” in ji ɗaya daga cikin fasinjojin.

Babu wani martani a hukumance daga kamfanin jirgin a daren jiya.

Ka zalika mai magana da yawun hukumar kula da filin jirgin sama FAAN, Mrs. Faithful Hope-Ivbaze, ta ce ba ta da masaniya game da lamarin.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa, dole ne a soke tashin jirgin saboda matsalolin fasaha da jiragen kamfanin suka samu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here