Yajin aiki: ƙungiyar NLC ta bai wa gwamnatin tarayya kwanaki 21 wajen warware matsalolin ASUU, NASU da sauran ƙungiyoyi

NLC President Wabba
NLC President Wabba

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta shiga tsakani kan rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin kwadago na manyan makarantu da ya gurgunta harkokin jami’o’i.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta ba gwamnatin wa’adin kwanaki 21 da ta warware matsalolin da ƴaƴan ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da ƙungiyar ma’aikatan da ba malamai ba NASU da kuma koken mambobin ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’in Najeriya SSANU ke yi har ma da Ƙungiyar Ƙwararru ta Ƙasa NAAT.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban NLC, Ayuba Wabba, da babban sakataren majalisar zartaswar ƙungiyar, Emmanuel Ugboaja suka sanya wa hannu ranar Larabar makon nan a Abuja.

Bayan ganawa da shugabannin kungiyoyin da abin ya shafa, Wabba ya nuna matukar damuwarsa kan yadda gwamnati ta kasa cika yarjejeniyar da ta tattaunawa da su a shekarar 2009.

Ya bayyana cewa bayan ƙarewar wa’adin kungiyar ta NLC za ta yanke hukunci kan mataki na gaba idan gwamnati ta gaza magance matsalar cikin wa’adin.

Ƙungiyar ta kira taro na ƙungiyoyin ilimi masu alaƙa da lamarin a ranar 12 ga Afrilu 2022.

Babban maƙasudin taron shi ne ɗaukar rahotonni game da yajin aikin da ke gudana a jami’o’in Najeriya.

Taron wanda shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya ya jagoranta ya samu halartar shugabannin kungiyoyin kamar haka:

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU);

Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimin da ba na Ilimi ba (NASU);

Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU); kuma

Ƙungiyar Ƙwararru ta Ƙasa (NAAT).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here