Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) shiyar Kano, ta kaddamar da “Operation Sharar Mafaka”, inda ta kama mutum 52 da ake zargi a wuraren sayar da miyagun kwayoyi a fadin kwaryar birnin na Kano.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar shiyar Kani, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa “Sharar Mafaka” na nufin “Clearing Hideouts” ko “Sweeping Safe Haven” a Turance.
Kwamandan hukumar a Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, ya ce: “An kaddamar da aikin ne da nufin kawo karshen wuraren rarraba miyagun kwayoyi da maido da tsaro ga al’umma.
“A ranar 27 ga Afrilu, an kaddamar da hare-hare inda aka kai hari wurare sama da 20 da aka gano ana sayar da miyagun kwayoyi, lamarin da ya haifar da kama mutane da kwace kayayyaki masu yawa cikin kwanaki biyu.
“A ranar 27 ga watan Afrilu, jami’anmu sun kai samame Filin Idi, Tashar Rami, Fagge, Mahauta da Farm Centre, inda aka kama mutum 15 da ake zargi, kuma aka kwato miyagun kwayoyi da makamai masu yawa.” Inji kwamandan.
Ya kuma kara da cewa, “A ranar ta biyu kuma, 28 ga watan Afrilu, an kara kai samame a Gadar Sama ta Hotoro, Tashar Mota ta Mariri, Ramin Jirga Tishama, Tashar Mota ta Yankaba da Sakatariyar Audu Bako, lamarin da ya haifar da kama mutum 16 da ake zargi, ciki har da mata uku, da kuma kwato miyagun kwayoyi iri-iri da makamai da aka kera a gida.”
Kwamandan ya kara da cewa adai ranar, hukumar ta gudanar da karin ayyuka a Kwanar Ungogo, Titin Jajira, Tudun Bojuwa da wasu sassan Sabon Gari, lamarin da ya haifar da kama wasu mutum 21 da ake zargi, ciki har da mace daya.
“Za mu ci gaba da tarwatsa matattarar masu aikata muyagun laifuka, mu kama su da kwayoyin har sai mun tabbatar da mun tsaftace ko’ina.” Inji shi.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa hukumar cikakken hadin kan da ya kamata a yakin da take da shaye-shaye da safarar muyagun kwayoyi, har sai an tabbatar tsaftace hanyoyi.











































